fbpx
Friday, May 27
Shadow

“A duk lokacin da mutane suka kunna talabjin a Najeriya labarin da ake ji shi ne kan tashin hankali.”>>IBB

Tsohon shugaban Najeriya Ibrahim Badamasi Babagida ya nuna matuƙar damuwa dangane da halin da kasar ta tsinci kanta na taɓarɓarewar tsaro.

A wata hira da ya yi da BBC, Ibrahim Babangida ya ce yanzu akwai bukatar ‘yan kasar su dage da addu’o’in samun sassauci daga kashe-kashen da suka yawaita a sassan kasar.

Sannan ya jaddada bukatar bai wa jami’an tsaro hadin-kai don kakkaɓe ɓata-gari.

Tsohon shugaban ƙasar na mulkin soja, ya ce ya wajaba a janyo hankali a’lummar kasar da su nuna jajircewa da yin addu’oi da kyakkyawan fata ga Najeriya saboda ‘yan kasar ba su da wata kasa bayan ita.

“Tilas mu tabbabatar mun yi wa kasarmu addu’a domin neman hadin-kan kasa da al’umma baki daya,” in ji shi.

IBB ya ce ya yi wannan kiran ne saboda yadda ake samun karuwa da yawan tashe-tashen hankula a kasar.

Sai dai ya ce duk da cewa gwamnatin kasar da sauran mutane na kokari wajen shawo kan matsalar amma wani lokaci abin akwai ban tsoro.

“Ya kamata mu koma ga Ubangiji mu roƙe shi ya yi mana afuwa ya kuma kawo mana ƙarshen wadannan abubuwa,” a cewarsa.

Sai dai kuma tsohon shugaban kasar Najeriya ya ce akwai bukatar ganin gwamnatin ta dauki matakin gudanar da taron yin sulhu domin a ba wadanda suke ganin an yi musu laifi damar magana da kuma sasantawa.

Ya kara da cewa wannan mataki yana tasiri sosai wajan dawo da zaman lafiya a wasu ƙasashen duniya

IBBC dai na ganin akwai bukatar a samu wani wuri da jama’a za su taru su kawo koke-kokensu kuma gwamnati ta dauki matakin da zai tabbatar da cewa hankalin mutane ya kwanta kuma za su yi hakuri dan kasar ta ci gaba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.