Matasan Arewa sun gayawa jam’iyyar APC cewa suna son ta fitar da dan takarar shugaban kasa na 2023 a jam’iyyar daga Arewa.
Matasan sunce suna son a Arewar ma a fitar da dan takarar daga Arewa maso yamma.
Kungiyar matasan data fitar da sanarwa a Abuja tace duk wani kokarin kai mukamin zuwa wani yanki ba na Arewa maso yamma ba yana da hadari.
Shugaban kungiyar matasan, Mohammed Abubakar (Esq) yayi kiran cewa, suna son a tsayar da ko dai gwamna Badaru na jihar Jigawa, ko kuma Alhaji Sani Yariman Bakura wannan takara.