fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

A kafar sata zumunta kadai aka san Peter Obi domin jam’iyyarsu ko dan majalissa bata da shi, Atiku yace baya fargabar Labour Party

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa a kafar sada zumunta kadai aka san dan takarar shugaban kasa na Labour Party, wato Peter Obi.

Kuma yawancin al’ummar arewacin Nakeriya kashi 90 cikin 100 basa amfani da kafafen sada zumunta sosai, saboda haka baya shakkar jam’iyyar Labour Party.

Atiku ya kara da cewa Peter Obi bashi da wani babban tarihi a siyasar Najeriya wacce har zata iya saka shi yayi nasarar lashe zaben shugaban kasa.

Kuma a karshe tsohon mataimakin shugaban kasar yace jam’iyyar Labour Party batada gwamna, sanata da kuma da majalissa saboda haka baya shakkar su.

Leave a Reply

Your email address will not be published.