fbpx
Thursday, July 7
Shadow

A karin Farko, Atletico Madrid ta yi nasara akan Barcelona:Bidiyon Kuskuren da Golan Barca ya tafka da ya jawo aka ci su kwallon

Atletico Madrid ta yi nasara akan Barcelona a wasan da suka buga jiya da ci 1 me ban haushi. Yannick Carrasco ne ya ciwa Atletico Madrid kwallonta bayan dawowa daga hutu Rabin Lokaci.

 

Wannan nasara ta Atletico Madrid akan Barcelona itace irin ta ta farko cikin kusan sama da shekaru 10 da suka gabata.

 

Nasarar ta baiwa Atletico Madrid damar komawa ta 2 a saman teburin gasar La Liga da maki 20, daidai dana Real Sociedad dake saman Teburin.

 

Golan Barcelona, Marc Andre ter stergen ne ta tafka gagarumin kuskuren da yasa aka ci kungiyar kwallo, inda ya fito cikin fili ya bar ragarsa.

 

Karanta wannan  Kungiyar PSG ta kori kocinta Maurizio Pochettino

Sau 5 kenan golan yana kuskuren da ke kaiwa ana cin kungiyar tasa tun daga watan Afrilun 2019 da ya gabata zuwa yanzu. A gasar La Liga,  babu golan da ya kaishi aikata irin wannan shirmen, a tsakanin wannan lokaci da aka ambata.

 

Saidai bayan wasan, Kocin Barcelona,  Ronald Koeman ya dauki alhakin rashin nasarar.

 

Kalli Bidiyon kwallon da aka ci:

 

Sauran wasannin ds aka buga a jiya, sune wands Real Madrid ta Villarreal suka tashi 1-1, sai Sevilla da tawa Celta Vigo 4-2, sai kuma.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.