Alkaluman da hukumar kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC ta fitar a jiya, Litinin sun bayyana cewa ba’a samu karin wanda suka kamu da cutar ba a jihar Legas, kwana daya bayan da aka samu mutane 70 da suka kamu da cutar.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Akin Abayomi ya tabbatar da hakan inda yace saidai mutane 2 sun mutu sanadin cutar.
Yace daya daga cikin wanda suka mutun, namijine dan shekaru 45 wanda bai dade da dawowa daga kasar India ba.
Dayar kuma ta macece me shekaru 36 wadda bata da tarihin fita kasar waje ko ma’amala da wani wanda ya fita kasar waje ba.
☑️The second death involved a 36 year old Nigerian🇳🇬; female with severe underlying health condition. She had no history of travel or contact with any #COVID19 confirmed case.
☑️Total number of #COVID19 related deaths in Lagos now stands at 16@drobafemihamzat @JokeSanwoolu
— Prof. Akin Abayomi (@ProfAkinAbayomi) April 21, 2020
Jimullar wanda suka mutu sanadiyyar cutar Coronavirus/COVID-19 a jihar 16 kenan zuwa yanzu.