Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta sha kashin ban mamaki a hannun Atletico Madrid data bita har gida,Anfield ta mata ci 3-2 a daren Laraba.
Liverpool ce ta fara cin kwallo ta hannun Wijnaldum wadda ta so ta makale, ta kara kwallo ta 2 ta hannun Firmino.
Saidai Atletico Madrid ta farke duka kwallaye 2 ta hannun Llorente inda ta kara kwallo ta 3 ta hannun Morata.
Wannan na nufin Liverpool ta sha kashi da jimullar kwallaye 4 kenan a hannun Atletico Madrid, Gida dawaje.
Wannan ne karon farko da aka fitar da Liverpool daga gasar Champions League a matakin kungiyoyi 16 da suka rage a gasar cikin shekaru 14 da suka gabata.
Tun bayan da Wani yaro dan shekaru 10 magoyi bayan Manchester United ya yiwa Liverpool baki kan cewa ba zata kara tabuka abin a zo a gani ba kungiyar ke ta kara kasa.