A Karon Farko Gwamna Zulun Ya Sha Ihun ‘Ba Ma So’, ‘Ba Ma Yi’ A Jihar Borno
Daga Abubakar A Adam Babankyauta
Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umaru Zulum ya sha ihun ‘ba ma so’, ‘ba ma yi’ a lokacin da yake fadawa al’ummar garin Maiduguri da su zabi Tinubu a matsayin shugaban kasa.
Hakan yana nuna cewa akwai alamun tallar Tunubu za ta yi wuyan gaske a yankin Arewa. Domin idan har metamen Borno za su yi wa Gwamna Zulum ihun ba ma so, ba ma yi akan Tinubu, to wane mutum ne zai tallata Tinubu ya kai labari a yankin Arewa?