fbpx
Monday, August 15
Shadow

A karshe dai abokin takarar Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya bayyana

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu na shirin bayyana abokin takararsa kwanan nan.

Tinubu ya bayyana cewa zai zabi abokin takarar nasa ne tsakanin jihar Kaduna, Kano da kuma Borno, yayin da kuma aka samu labari daga majiya mar karfi cewa zai zabi gwamna Zulum na Borno ne ko kuma Sanata Kashim Shettima.

Yayin da majiyar ta kara da cewa shi gwamnan jihar Kaduna, El Rufa’i ya janye nasa ra’ayin duk da cewa yana cikin manyan mutanen da suka taimakawa Tinubu ya lashe zaben fidda gwani na APC.

Karanta wannan  Zamu fara baiwa talakawa miliyan 40 tallafin naira dubu biyar a kowane wata, cewar gwamnatin tarayya

Tinubu zai bayyana abokin takarar nasa ne kafin wa’adin da hukumar zabe tasa masu na ranar 15 ga watan Yuli ya cika.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.