fbpx
Friday, August 12
Shadow

A karshe dai hukumar ‘yan sanda ta damke jami’anta da suka lakadawa wata mata dan banzan duka kan taje neman yaronta da suka kama a jihar Osun

Hukumar ‘yan sanda ta damke jami’anta da suka lakadawa wata mata Blessing Mba dan banzan duka a ofishinsu kan taje naman yaronta dan shekara 15.

Blessing Mba taje neman yaron nata ne ofishin ‘yan sandan bayan ya jima bai dawo gida ba, amma sai shigabansu smya umurce su dasu lakada mata duka.

Kuma yaron nata na hannun su sun rike shi. Mai magana da yawun hukumar ta jihar, Yemisi Apolola ce ta bayyana cewa za’a kama jami’an sannan a cigaba da bincike kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.