Kungiyar Manchester United ta amincewa tauraron dan wasanta Ronaldo ya sauya sheka a wannan kakar amma da sharadi guda.
Ronaldo na son barin kungiyar ne don bata cancanci buga gasar zakarun nahiyar turai ba a kaka mai zuwa, kuma yanzu da yiyuwar ya koma Atletico Madrid.
Wanda hakan yasa Manchester tace masa to ya sabunta kwantirakinsa sai ta bayar dashi aro yaje ya buga gasar zakarun nahiyar turai sai ya dawo.
Inda take sa ran itama kafin ya dawo zata cancanci buga buga gasar tunda abinda yake so kenan.