Tsohon na hannun damar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amince ya goyi bayan Tinubu.
Yace an yi wannan alkawarine a shekarar da shugaba Buhari ke neman zama shugaban kasa bayan da yayi kokarin daukar Tinubu a matsayin mataimakin shugaban kasa amma hakan bata faru ba.
A hirarsa da Punchng, Buba Galadima ya bayyana cewa, amma ga dukkan alamu wannan alkawari da shugaba Buhari ya dauka yana neman Karyashi.