Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nesanta kansa da maganar marawa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan baya ya tsaya takarar shuhaban kasa a jam’iyyar APC.
Wata majiya daga fadar shugaban kasar, ta gayawa Jaridar Independent cewa, shugaba Buhari ya hana yada hotunan ganawarsa da tsohon shugaban kasar.
Wannan mataki ya daukeshi ne dan kada a rika ganin kamar yana son marawa Goodluck Jonathan baya game da maganar takarar shugabancin Najeriya.
Wasu na kusa da Buhari ne ciki hadda wani gwamnan Arewa ke ta kokarin ganin Tsohon shugaban kasar, Goodluck Jonathan ya dawo APC ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023.
Saidai a hukumance babu wata alama da ta nuna cewa, Jonathan ya koma APC duk da wasu Filani sun sai masa Fom din takara.