Rahotanni daga fadar ahugaban kasa, Muhammadu Buhari na cewa, shugaban na goyon bayan Mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo ya gajeshi.
Wani hadimin shugaban kasar ne ya gayawa kafar jaridar Daily Independent haka.
Majiyar tace shugaba Buhari na goyon bayan Osinbajo ne saboda yanda ya kasance yana tare da shugaba Buhari da suka fara aikin gina kasa kuma yana tsammanin zai ci gaba.
Shugaba Buhari kuma ya ga yanda a lokuta da dama Farfesa Yemi Osinbajo ya rike ragamar Najeriya a lokacin da baya nan.
ALLAH yasa she mafi alkairi ga yan NIGERIA