fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

A Karshe, Trump Ya Cika Alkawari, Ya Aiko Da Na’urorin Iska, Wato Ventilators Guda 200 Zuwa Nijeriya

Trump, a zantawarsa ta wayar tarho da Shugaba Muhammadu Buhari a watan Afrilu, ya yi alkawarin goyan bayan martanin Najeriya ga COVID-19 ta hanyar aikewa da na’urar ventilator.

Na’urorin sun isa Najeriya watanni biyar bayan shugaban na Amurka ya yi alkawarin.
Yayin karbar na’urorin guda 200 a madadin gwamnatin tarayya daga Hukumar Raya Kasa da kasa ta Amurka (USAID) a wani bikin da aka yi a Abuja ranar Talata, Ministan kiwon lafiya, Osagie Ehanire, ya ce abubuwan kiwon lafiya suna da matukar muhimmanci don ceton rayukan mutanen da suka kasance da mummunar cutar ta COVID-19.
Ministan ya ce rayuwa ta canza ga ‘yan Najeriya tunda aka fara samun masu cutar corona a watan Fabrairu.
“Wannan gudummawar ta kunshi na’urorin iska guda 200, wanda kuma kamar yadda muka sani yanzu, muhimmin bangare ne na dabarun bada agaji don ceton rayukan mutanen da wannan mummunar cuta ta kama” in ji shi.
“Tabbas za su yi amfani ga jama’ar Najeriya kuma ina son isar da sakon godiya ga Shugaba Muhammadu Buhari, Shugaban tarayyar Najeriya da kuma gwamnatin Najeriya ga Shugaba Donald Trump da Gwamnatin Amurka don wannan abin karimcin sada zumunci.
“Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, da jami’inta na kiwon lafiya, Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC), sun mayar da hankali don magance kalubalen.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Hotuna: Kungiyar kiwon lafiya ta kaiwa shugaba Buhari ziyara a fadarsa

Leave a Reply

Your email address will not be published.