Mai neman takarar dan majalisar Birnin Gwari a jihar Kaduna, Alhaji Abdulra’uf Zubairu ya baiwa masu tafiye tafiye shawar cewa su kauracewa hanyar karamar hukumar zuwa wani lokaci.
Ya bayar da wannan shawarar ne biyo bayan harin da ‘yan bindiga suka kai babbar hanyar a ranar talata 31 ga watan Mayu, inda suka tafi da dunbin mutane cikin jeji.
Kuma yace kwanaki hudu da suka gabata ‘yan bindigar sun takurawa manoma da sauran al’umma sosai, saboda haka ne yake bayar da shawara a kauracewa hanyar kafin a samu sauki matsalar tsaro.