fbpx
Thursday, August 18
Shadow

A koda yaushe kungiyar PSG tana maraba da manyan wasan tamola na duniya>>Sabon kocin PSG

Kungiyar Paris tama harin siyan kaftin din Barcelona, Messi da kuma da kuma dan wasan tsakiya na kungiyar Tottenham Dele Alli duk da cewa dai Spurs ta bayyana cewa ba zata siyar da Alli ba kuma ba zata bayar da shi aro ba a wannan watan.

Tauraron dan wasan Barcelona Lionel Messi ya samu damar fara tattaumawa da wasu kungiyoyin dake harin siyan shi, yayin da kwantirakin shi zai kare nan da 30 ga wata yuni mai zuwa.

Kuma sabon kocin kungiyar Paris Saint German wanda ya maye gurbin Thomas Tuchel, Mauricio Pochettino ya bayana cewa akoda yaushe kungiyar PSG tana maraba da manayan yan wasan tamola na duniya, wanda hakan yake nufin cewa har yanzu dai kungiyar tana harin siyan Messi da kuma Alli.

Leave a Reply

Your email address will not be published.