fbpx
Thursday, December 7
Shadow

A kullun ta Allah, ana sace danyan mai a Najeriya na sama da Biliyan 8.5>>Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta koka da cewa ana sace danyen man Najeriya na Biliyoyin naira a kullun.

 

Babban dan kasuwa, Tony Elumelu ya bayyana cewa sana da kaso 90 na danyen man Najeriya saceshi ake.

 

A yayin ganawa da karamin ministan man fetur, Timipre Sylva a gidan talabijin na kasa a wani shiri me suna eagle eye, an tambayeshi shin ya gaskiyar wancan ikirari na Tony Elumelu?

 

Sai yace shi Tony Elumelu yana amfani da wani bututu ne da ake cewa TNP wajan safarar kayansa.

 

Kuka shi wannan bututu ne aka fi kaiwa hari dan satar danyen mai shiyasa yake magana, yace dan haka yana magana akan abinda ya sanine.

 

Yace amma bashi da hurumi ko masaniyar da zai yi magana akan gaba dayan bututun man da gwamnatin tarayya ke amfani dashi.

 

Da aka tambayeshi amma shi yana ganin kamar ganga nawa ake sacewa a Najeriya? Sai ya kada baki yace bai da takamaimai alkaluman ganga nawa ake sacewa amma dai yasan zai iya kai ganga 200,000 a kullun wataran kuma ya canja.

 

Hutudole ya lissafa farashin wannan danyen man da ake sacewa ta hanyar amfani da farashin man Brent wanda shine ake lissafa danyen man Najeriya dashi.

 

A daidai lokacin wallafa wannan labari, farashin danyen man Brent yana kan $102.78 akan kowace ganga, kamar yanda shafin Yahoo finance ya ruwaito.

 

To fan sanin farashin danyen man da minista Timipre Sylva yace ana sacewa, sai mu buga 200,000 sau 102.78

Karanta wannan  Shugaban kasa, Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima zasu kashw Naira Biliyan 15 wajan Tafiye-Tafiye a shekarar 2024

 

Watau 200,000x$102.78

 

Hakan zai baka $2,556,000, watau sama da dala miliyan biyu da rabu kenan a kullun.

 

To nawane wadannan kudin idan aka mayar dasu zuwa Naira?

 

A daidai lokacin wallafa wannan labari, farashin da ake sayan kowace dala daya a hukumance shine N415.65.

 

Dan haka $2,556,000xN415.65=8,544,101,400.

 

Watau darajar kudin danyen man da ake sacewa a Najeriya a kullun ya kai sama da Naira Biliyan 8 da rabi.

 

Sylva yace mutanensu na Naija Delta na alakanta satar sanyen mai da hakar ma’adanai ta haramtacciyar hanya da ake yi a Arewa.

 

Yace amma sam ba daya bane, yace a Arewa, masu hakar ma’adanai ta haramtacciyar hanya na amfani da kayan aiki su hako ma’adanan ne a karkashin kasa, yace su kuma masu satar danyen mai suna kaiwa bututun man gwmanati datake amfani dashi harine.

 

Yace kuma hakan na matukar lalata rayuwar matasa wanda daga baya suke komawa masu garkuwa da mutane.

 

Yace ya kamata mutanensu su canja tunanin kwanciya a gida ana samun kudi ta hanyar satar danyen mai.

 

Yace kuma gwamnati kamata yayi ta rika kama masu laifin ba wai rufe bututun da ake satar danyen man ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *