Shugaban sanatoci Ahmad Lawal ya bayyana cewa a matsayin dan takarar jam’iyyar APC zai yiwa ‘yan Najeriya magana a duk sanda ya tashi isar masu da wani sako daga yau.
Lawal ya bayyana hakan ne bayan an kammala tantance shi a matsayin mai neman takarar shugabancin Najeriya a jam’iyar APC a jihar Abuja.
Inda yace sun tambaye shi tanbayoyi masu ma’ana sosai kuma a matsayin dantakarar jam’iyyar suka tantance shi ba wai mai neman zama dan takararta ba.