fbpx
Thursday, August 18
Shadow

A Mota muka je katsina daga Abuja>>Martanin Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad bayan da aka zargeshi da zuwa wajan Bikinsa da jirgin shugaban kasa

Sahara Reporters ta walafa hotuna hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad inda ta bayyana cewa yayi amfani da jirgin shugaban kasa wajan zuwa bikinsa a Katsina.

 

Ta zargi shugaban kasa, Muhammadu Buhari da aikata ba daidai ba da ofishin nasa ta hanyar barin bashir din yayi amfani da jirginsa.

 

Saidai a martaninsa, Bashir yace ba a jirgi ya je Katsina ba, a mota suka je shi da abokanan sa kuma a mota suka wuce Kano, sannan kuma a mota zasu koma Abuja bayan kammala biki.

 

Yace wadannan hotunan an daukesu ne a yayin da shi da abokansa suka je tarbar wakilan da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tura wajan bikin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Gadon Boko Haram mukayi a wurin PDP kuma kuma yanzu mun kusan babu su a doron kasa duk mun hallaksu, cewar gwamnatin tarayya

Leave a Reply

Your email address will not be published.