fbpx
Monday, March 1
Shadow

A raba Auren mu:Mijina na Amfani da Sihiri wajan yin Jima’i dani, idan ya fara sai na suma>>Mata ta gayawa Alkali

Wata mata ta maka mijinta a kotu inda take neman kotun ta raba aurensu saboda yana amfani da Sihiri wajan yin Jima’I da ita.

 

Matar tace a duk sanda mijin nata ke Jima’i da ita sai ta suma. Matar me suna Bukola Ejalonibu ta bayyana cewa, idan ta suma yawanci sai an kaita Asibiti.

 

Kamfanin dillancin labaran Najeriya,NAN ya ruwaito cewa matar ta shigar da karar ne a kotun Mapo dake jihar Oyo. Saidai mijin nata, Kolawole ya karyata zargin da ta masa inda yace bata da godiyar Allah duk da abinda yake mata.

 

Mai shari’a, Ademola Odunade ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya raba auren tare da baiwa matar rikon yara 2 da suke dashi sannan ya bukaci mijin ya rika bata Dubu 10 duk wata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *