Gwamnatin tarayya ta amince da amfani da BVN wajan gano masu Bukatar tallafin da take bayarwa ga ‘yan Najeriya.
Gwamnatin dai zata fadada yawan mutanen da take baiwa tallafinne kamar yanda ministar tallafawa mutane da da kula da Ibtila’i, Sadiya Umar Farouk ta bayyana.
Ta bayyana hakane a ranar Talata wajan tattaunawa da manema labarai da kwamitin shugaban kasa dake yaki da Cutar Coronavirus/COVID-19 yayi.
Sadiya ta bayyana cewa amfani da fasahar zamani wajan gano wanda ke da bukatar tallafin zai fi zama cikin sauki da kuma a bayyane babu wani boye-boye.
Tace zasu yi amfani da BVN da kuma lambobin waya wajan gano masu bukatar.
Jigo a jam’iyyar APC,Bola Ahmad Tinubu dai ya baiwa gwamnatin shawarar amfani da BVN a baya.
Saidai gwamnatin tace zata yi amfanine da masu saka Naira 100 a waya da kuma masu kasa da Naira Dubu 5000 a Asusun Ajiyarsu, abinda ya jawowa gwamnatin caccaka.
Amma wannan sabon matakin da gwamnatin ta dauka kamar ta lashe amantane.
Muharyanzu bamugani akoryaba
allah yasa mu amfana da wannan tallafin
Anjima anaruwa kasa na shanyewa,wannan yaudara ta ishemu
A gaggauta aiwatar da tallafin, don talakawa na Cikin wani hali.wannan tun tuni ya kamata ku aiwatar kamar yadda Tinubu ya ba da shawara.
Allah yasa abun ya kai ga talaka. A zamfara shiru a ke
ALLAHU yasa haka kuma indai anyi haka to annemi a tallafawa ta lakawa
Mudai sedai muce toh
Kullum haka muke ji, amma har yanzu malam talaka bai sha roman dumurakadiyyaba
Allah yasanyawa Nigeria albarka yakuma tonawa munafukan kasa asiri amin
Allah yasa mudache
wallahi tallahi tunda aka fara lockdown ban kara zuwa kasuwa ba wallahi ko tsinke babu akan teburi na na kasuwa kuma wallahi ko naira biyar bani da ita wacce zan dora jari da ita kuma ban san inda tallafin nan na gwamnati yake zuwa ba kuma bansan ta yadda ake samunsa gashi bani da account din banki wannan wane irin tallafi ne da baya zuwa inda ya dace?
Nidai aganina suna fadane kawai
Yaudara kawai da rashin tausayi amma kwai ranar saka mako, ranar da gaskiya zatayi halinta
Allah ya sa afara da wuri
Am INA mai roqon wanan gwamnati mai albarka da ta kara jajircewa da yanda ta saba wanan taimako da ta taimaka walahi mutane na cikin fatara ta yinwa da rashin abinci Wanda sanadiyar hakan walahi wasu sun rasa rayukansu.
Allah Yasa Temakon Ya’isa Inda Yadace