Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, shi a yanzu haka yana da kuri’u Miliyan 11.
Ya bayyana hakane ga wakilan jam’iyyar PDP dan su zabeshi a matsayin dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar.
Atiku ya bayyana hakanne a gawar da suka yi a Abuja.
Hakan na zuwane bayan da wasu magoya bayan Tinubu suka fito suka ce zasu kawo mai kuri’u Miliyan 14 daga yankin Inyamurai.
A zaben shekarar 2019, Atiku Abubakar ya samu kuri’u kusan Miyan 11, watakila yana maganane akan wadancan kuri’un.