fbpx
Thursday, August 18
Shadow

A yanzu Najeriya ta kai Kololuwar yaduwar Coronavirus a tsakanin Al’umma>>Gwamnatin tarayya

Sakataren gwamnatin tarayya wanda kuma shine shugaban kwamitin shugaban kasa dake yaki da cutar Coronavirus/COVID-19,  Boss Mustapha ya bayyana cewa, A yanzu Najeriya ta kai matakin kololuwa na yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19 tsakanin al’umma.

 

Ya bayyana hakane a jiya,Lahadi a fadar shugaban kasa bayan gawar da suka yi da shugaban kasar.

Yace cikin kananan hukumomi 774 da ake dasu a Najeriya guda 20 ne ke da kaso 60 na yawan masu cutar Coronavirus/COVID-19 da ake dasu.

 

Ya kuma bada tabbacin cewa jihohine zasu koma kula da masu cutar nan gaba

Leave a Reply

Your email address will not be published.