fbpx
Monday, August 15
Shadow

A yau aka gabatar da tsohon mataimakin shugaban sanatoci, Ekweremadu da matarsa a kotun Landan, inda ake sa ran watakila a cigaba da sauraron shari’ar a Najeriya

A yau ranar alhamis aka gabatar da tsohon mataimakain shugaban sanatoci a koton Landan kan zarginsa da ake yi na safarar sassan jikin dan adam.

A cikin wannan watan ne aka kama tsohon mataimakin shugaban sanatocin, Ekweremadu tare da matarsa Beatrice a kasar Landan.

Kuma sun kasance a hannun hukumar ‘yan sandan Landan tun bayan da aka kamasu da laifi  kasar, inda a yau mai gabatar da kara a kotun magistare yace yaron da suka kawo Landan don ya ba diyarsu hantarsa dan shekara 15 ne.

Channels sun bayyana cewa an daga sauraron karan izuwa bakwai ga watan Yuli a kotun ta magistare, domin a baiwa shugaban lauyoyin Landan damar yin nazarai akan mayar da shari’ar Najeriya ko kuma a cigaba a Landan din.

Leave a Reply

Your email address will not be published.