A yau ne ake sa ran Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo zai bayyana a hukumance cewa zai tsaya takarar shugabancin Najeriya.
A jiya, Lahadi yayin tarin shan ruwa a fadar shugaban kasa, Osinbajo ya bayyanawa gwamnonin da suka halarci taron aniyarsa ta son gadar shugaba Buhari.
Wasu Rahotanni sun bayyana cewa, ba za’a yi wani taro na musamman ba yayin bayyana aniyar ta Osinbajo, kawai zai dauki bidiyo ne ya watsa.