A yau, Asabar, 13 ga watan Fabrairu, shekaru 45 kenan da rasuwar tsohon shugaban kasa, Janar Murtala Muhammad.
An kasheshi ranar Juma’a, 13 ga watan Fabrairu na shekarar 1976 akan hanyarsa ta zuwa aiki.

Ya shafe kwanaki 200 a matsayin shugaba Najeriya kamin a masa wannan kisan gilla.