A yau take ranar zaben gwamnan jihar Ekiti yayin da jam’iyyar mulki ta APC, PDP da SDP ne manyan jam’iyyun da zasu fafata wurin neman kujerar.
Inda APC ta tsayar da Biodun Oyebanji, sai PDP ta tsayar da tsohon shugabanta na jihar watau Bisi Kolawole yayin da ita kuma SPD ta tsayar da tsohon gwamnan jihar, Segun Oni.
Tun shekarar 1999 APC da PDP ne kadai ke mulkar jihar kuma yau za a gudanar zaben ne a kananun hukumi 16 dake jihar, kafin a sanar da wanda yayi masara bayan an kammala.