A yau, Alhamis ne ake sa ran Bola Tinubu dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC zai dauki mataimakinsa.
Bola Tinubu dai na tantamar daukar musulmi ko kirista saboda tunanin yanda zai ci zabe.
Saidai jam’iyyar ta APC ta bayyana cewa, daga yankin Arewa maso gabas ne Bola Tinubu zai dakko mataimakin nasa.
Wani jigo a tafiyar Tinubun ya bayyana cewa, PDP na tsoron Bola Tinubu ya dauko mataimaki musulmi.
Ana ganin dai idan ba Musulmi Bola Tinubu ya dauko daga Arewa ba, da wuya ya ci zabe.