Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmad Tinubu zai kaddamar da tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa yau.
Tsohon gwamnan jihar Legas din zai kaddamar da shine a Musa Yar Adua dake babban birnin tarayya Abuja.
Tinubu na shan suka sosai kan zabar Kashim Shettima daya yi a matsayin abokin takarar nasa kasancewar su Musulmai ne gabadaya.
Amma duk da haka yayi burus yaki canja shi kuma yau zai kaddamar dashi kamar yaddda jam’iyyar APC ta bayyana a jiya ranar lalata.