fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

A yau wa’adin da Dortmund ta sakawa United na siyan Sancho ya cika dan haka yayi Atisaye tare da ‘yan wasan Dortmund domin

Burin Manchester United na siyan Jadon Sancho daga kungiyar Dortmund yaja baya bayan Dortmund ta saka sunan dan wasan a cikin jerin yan wasan ta da zasu yi tafiya izuwa kasar Switzerland domin su fara gudanar da atisayi kafin a fara buga kaka mai zuwa.

Manchester United ta dauki tsawon wasu watanni tana farautar dan wasan kuma kiris ya rage ta siya Sancho a makon daya gabata, amma sai dai yanzu wa’adin da Dortmund ta saka masu na siyan dan wasan ya cika. Kungiyar Bundlesligan taso United ta kammala siyan dan wasan kafin su fara atisayin amma sai dai yanzu sun riga da sun saka sunan Sancho a cikin yan wasan da suka yi tafiya izuwa Switzerland ranar litinin.
Kuma hakan ka iya sa yanzu United dole ta biya makudan kudaden da Dortmund ta sakawa dan wasan na euros miliyan 108 idan har tana son siyan shi. Masoyan United har sun fara tunanin cewa kungiyar ta kusa siyan Sanco a karshen wannan makon bayan sun ganshi a wani biki a kasar Landan,amma Dortmund ta gaggauta mayar masu amsa bayan sun ga Sancho yayin da suke cewa;
Abin da Sancho yayi ba wani abu bane saboda mafi akasarin yan wasa suna komawa gida kafin a fara gudanar da atisayin sabon kaka, kuma hotunan da yayi basu saba dokar korona ba saboda haka zai koma kungiyar shi. Dan wasan mai shekaru 20 ya amince zai koma United amma daya daga cikin shuwagabbanin Dortmund Watze ya bayyan ranar laraba cewa babu wata yarjejeniya tsakanin kungiyoyin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.