A yaune ake shirin tabbatar da ‘yar Najeriya, Ngozi Okonjo Iwaela a matsayin shugabar Cibiyar Kasuwanci ta Duniya, WTO.
Idan hakan ya tabbata, Ngozi zata zama mace ta farko daga Africa da ta samu wannan mukami.
WTO ta kira wani babban taronta wanda ake tsammanin a shine za’a tabbatarwa da Ngozi Mukamin.