Sunday, March 29
Shadow

A yayin da ake tsaka da yaki da Coronavirus/COVID-19, kungiyar malaman jami’a ta Tsunduma yajin aikin sai mama ta gani

Kungiyar malaman jami’a ta ASUU ta tsunduma yajin aikin Sai Mama ta Gani biyo bayan kin biya musu bukatunsu da gwamnatin tarayya ta yi.

 

A ranar Litinin, 9 ga watan Maris na shekarar 2020 ne kungiyar ta tsunduma yajin aikin gargadi na mako 2.

 

A wata sanarwa da shugaban ASUU, Fargesa Biondun Ogunyemi ya fitar ga manema labarai yace sun tsunduma yajin aikinne saboda rashin daukar mataki kan bukatunsu da gwamnati ta yi.

 

Matsalolin na ASUU sun hada da cika alkawarin data dauka da gwamnati da kuma maganar sabon tsarin biyan Albashi na IPPIS

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwx

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *