Babban dan sandan Najeriya da aka dakatar, mataimakin kwamishinan DCP Abba Kyafi ya roki kotu cewa ta bayar da belinsa.
Kyari ya roki kotun cewa ta bayar da belin nasa ne biyo bayan matsalar tsaron da kurkukun ke fama da dashi, inda har aka kai masu hari.
Ana zargin dan sadan ne tare da wasu abokan aikinsa da laifin safarar miyagun kaayoyi, kuma suma sum nemi kotun ta bayar da belin nasu amma daya daga cikinsu bai nemi wannan alfarmar ba.
Mai shari’a Emeka Nwite ya saka yace zai saurari wannan korafin nasu ranar laraba na belin da suka nema.