fbpx
Thursday, February 9
Shadow

ABIN A YABA: Wata Kirista Ta Baiwa Musulmai Gudummawar Siminti Buhu Hudu Domin Gina Masallaci

ABIN A YABA: Wata Kirista Ta Baiwa Musulmai Gudummawar Siminti Buhu Hudu Domin Gina Masallaci

Wata Kirista a garin Mararraba dake karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa ta bada gudummawar siminti buhu hudu don gudanar da ginin wani masallacin Juma’a da aka rushe domin sabunta shi.

Masallacin wanda ake yi wa lakabi da Masallacin Sani Zamfara (Zamfara Mosque) dake unguwar Tudun Wada a garin na Mararraba, dandazon al’ummar musulmai dake yankin ne suke fito a safiyar yau Asabar domin yin aikin gayya don ganin an soma dora tubalin gininsa.

Karanta wannan  NHRC Za Ta Binciki Ayyukan Sojoji A Arewa Maso Gabas Za a tabbatar da adalci kan duk yadda sakamakon binciken ya nuna.

Matar dai wadda kabilar Yarbawa ce, ta yi matukar shan yabo a wurin musulman unguwar bisa gudummawar bazatan da ta yi musu duba da cewa ba addininsu daya ba.

Daga Shafin Rariya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *