ABIN AL’AJABI: Wasu Mabarata Sun Ƙi Karɓar Sadakar Tsohuwar Naira 1000 A Kaduna
A yau Laraba ne wasu gungun mabarata suka ki amincewa da tsofaffin takardun kudi na Naira 1,000 da wani Basarake ya ba su a babbar hanyar Kano-road, dake Kaduna.
Majiyar Sahihiya ta rawaito cewa mabaratan su uku ne suka yi wa wani matashi birki a kan keken guragu a lokacin da ya sauka daga motar safa.
A lokacin da ya fahimci suna neman abin hannu, sai mutumin ya dauki takardar tsohuwar naira 1000 daga cikin jakarsa ya mika wa babban mabaraci daga cikin su. ukun.
Sai dai abin mamaki sunƙi karɓa cewar su, yanzu an daina karɓar tsohon kuɗi.