fbpx
Friday, July 1
Shadow

Abin da Buhari yayi ya matukar kadamu, Saikace ana Mulkin Soja, Zamu kaishi kotu>>Inji Gwamnonin Najeriya kan dokar da shugaba Buhari yayi ta baiwa bangaren shari’a da na majalisun jihohi damar cin gashin kansu

Gadukkan alamau dokar da shugaban kasa,Muhammadu Buhari yayi ta baiwa ‘yan majalisu da bangaren shari’a na jihohi damar cin gashin kansu baiwa gwamnonin Najeriya dadi ba.

 

Wasu gwamnonin sun bayyana cewa wannan lamari ya zo musu da matukar mamaki saboda akwai maganar da suke yi da fadar shugaban kasar wadda marigayi, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa,Malam Abba Kyari ke jagoranta akan baiwa ‘yan majalisar da vangaren jihohi ikon cin gashin kansu kuma ba’a cimma matsaya ba, kwatsam sai gashi suka ji wannan mataki.

Wasu gwamnonin sun bayyana cewa Kotu zasu kai shugaban kasar dan baida ikon yin wannan doka, sunce wannan irin matakin na mulkin soja ne.

 

Wasu gwamnonin da suka yi magana da TheNation sun bayyana cewa haka fa shugaba Buhari ya baiwa bangaren kananan hukumomi irin wannan cin gashin kai, abinda har yanzu basu gama farfadowa daga rudanin daya saka su ma amma kwatsam sai kuma ga wannan?

 

Wasu gwamnonin sun bayyana cewa ba lallai su tunkari shugaba Buhari kai tsaye akan wannan batu ba amma zasu dauki nauyin wasu kungiyoyin kare hakkin dimokradiyya dan su maka shugaba Buhari a kotu akan wannan batu.

Karanta wannan  Dalilin dayasa na yiwa Tinubu lakabi da Jagaban, Sarkin Borgu

 

Wani gwamna daga Arewa maso gabas ya shaidawa TheNation cewa maganar sasantawa akan wannan mataki da shugaban kasa ya dauka bata taso ba, Kotu kawai zasu makashi tunda dai ya dauki wannan mataki da yawa doka karan tsaye.

 

Gwamnonin sun bayyana cewa a wannan lokaci da suke kan fama da matsin tattalin arziki sanadin cutar Coronavirus/COVID-19 ba zasu amince da matakin na shugaban kasa ba.

 

Saidai wasu manyan Lauyoyin Najeriya sun goyi bayan shugaban kasar akan wannan mataki.

 

Femi Falana da tsohon shugaban kungiyar Lauyoyi ta Najeriya, Dr. Olisa Agbakoba sun ce shugaba Buhari yayi daidai akan wannan batu dan kuwa dama can kundin tsarin mulki ya tanadi baiwa ‘yan majalisar jihohi da bangaren shari’a na jihohin damar cin gashin kai.

 

Sun kara da cewa dama can gwamnoninne ke yiwa wannan doka karantsaye. Sun kara da cewa hakan zai samar da yanayin shugabanci me kyau.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.