Wani abin dariya ya faru a yau Asabar 2 ga watan Disamba, wasu matane, suna da kungiyarsu ta taimakawa kansu da kansu, sun raba mukamai a tsakaninsu, akwai shugaba, akwai sakatare, akwai PRO(watau me kula da huldar jama’a), dadai sauransu, sai suka nemi suga wani dan siyasa dan ya taimakawa wannan kungiya tasu.
Suka yi sa’a kuwa ya gayyacesu ofishinshi, bayan an gaisa, suka bayyanamai cewa su duka nan masu rike da mukamaine na kungiyar, sai ya bukaci su fadi sunayensu da kuma mukaman da suke rike dasu, suka fara tashi daya-bayan-daya suna gabatar da kawunansu.
Da aka zo kan PRO, sai ta tashi tace, sunana wance-wance…..sai ta dan tsaya, ta juya ta kalli abokan tafiyartata, tace, waini yama sunan mukamin nawa?…. kamin kowa ya bata amsa sai tace “Au nice ORT ta wannan kungiya”.
Nan kuwa kowa yace me zaiyi inba dariyaba, hadda shi dan siyasar da suka kaiwa ziyara, ya kasa hadiye dariyarshi saida ya dara.