fbpx
Saturday, March 25
Shadow

Abin Dariya:PDP tace zata yaki cin hanci fiye da APC idan taci zabe>>Gwamna Ahmad El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna. Malam Nasiru Ahmad El-Rufai yayi wani barkwanci akan wani alkawari da jam’iyyar PDP tayi akan cewa wai idan taci zabe zata yaki cin hanci da rashawa fiye da jam’iyyar APC.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Gwamnan yayi wannan barkwancine a dandalinshi na sada zumunta da muhawara inda yace:

“Barkwanin ranar Lahadi:”PDP tace zata yaki cin hanci da rashawa fiye da yanda APC ke yi a yanzu idan ta kwace mulki a zaben shekarar 2019 me zuwa. Domin kara samun labaran ban dariya aika PDP zuwa 419(zamba cikin aminci)”.

Tun bayan da ya wallafa wannan rubutune sai ya dauki hankulan mutane akayi ta mayar da martani iri-iri, wasu sunce wai ai babu banbanci tsakanin PDP da APC din wasu kuwa sun yarda da wannan magana da gwamnan yayi.
Mutane da yawa dai idan ana cikin magana wani zai yaudaresu kokuma zai mutu wani abinda ba daidai ba sukan ce “haba! kada ka mana PDP mana”.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Siyasa Kenan Sun Hadu A Air Port Gashi Suna Ta Wasa Da Dariya A Junan Su 🤣

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *