fbpx
Monday, August 15
Shadow

Abin Mamaki: An hada Kwado aure dan neman ruwan sama a kasar India kuma an samu ruwan

Wani abin mamaki ya faru a kasar Idiya inda aka hada kwadi aure.

 

Lamarin ya farune a yankin Gorakhpur na kasar.

 

Mutanen garin sun ce manoma na ta kukan babu ruwa suna son su yi shuka, dan hakane sai suka tuna da wata al’ada cewa, wai idan aka hada kwadi aure, za’a samu ruwan sama.

Sai kuwa aka hada wannan gagarumin biki inda mutane da yawa suka halarta. Jim kadan da kammala bikin kuwa sai ga ruwan sama.

 

An daura aurenne ranar 19 ga watan Yuli inda kuma ranar 20 ga watan aka ga ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.