fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Abin Sha’awa:Kalli yanda ake koyar da yaren Hausa a kasar China

A cikin wannan hoton bidiyon wasu mutanen kasar China ne zaune a aji ana koya musu yaren Hausa, wannan ba karamin abin alfahari bane ace yaren Hausa, wadanda ba Hausawa ba sun daukeshi da muhimmanci haka, har suka ware lokacinsu suna so si iyashi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Amma abin takaici wasu Hausawan basu dauki yaren nasu da muhimmanci ba, sai kaga waisu dole sai harshen aro, turancine abin alfahari a gurinsu, ta yanda wanda be iya turancin ba ko kuma yayi kuskure wajan yinshi ya zama abin dariya da nunawa a gari.
Tabbas mu a Najeriya Turanci ya zamar mana larura, amma irin muhimmancin da muka bashi yayi yawa, da ace zamu samu manya masu kishin yaren Hausa sosai da an saka manashi a cikin doka mun rika amfani dashi waja  ayyuka da koyarwa kuma da wallahi irin cigaban  da za’a samu ba kadan bane.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Tinubu ya gana da sarakunan gargajiya a fadarsa

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *