fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Abin takaici:Ji yanda talauci yasa kananan ‘yan mata ‘yan kasa da shekaru 20 karuwanci a jihar Bauchi

Kananan ‘yan mata ‘yan kasa da shekaru 20 na harkar karuwanci a jihar Bauchi kamar yanda rahoton jaridar The Nation ya ruwaito.

 

Lamarin na faruwane a bayan gari, wata unguwa dake bayan filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa dake jihar.

 

Bayan karuwancin, kananan ‘yan matan na kuma rayuwar shaye-shaye da ta saka rayuwarsu cikin halin barazana.

 

Gidan da yaran ke karuwanci kusan a boye suke, sai mutum yayi da gaske zai gane, kuma duk da suna karuwancin suna saka hijabi.

 

Jami’ai na kai samame anguwar amma da wuya suke samun kama kananan ‘yan matan dake karuwancin saboda sukan yi shiga irin ta kamala.

 

Wata me suna Chonda dake da shekaru 16 da wata itama da suke da shekaru daya sun bayyanawa jaridar cewa, samarinsu ne suka dirka musu ciki wanda daga baya suka shiga harkar karuwancin.

Karanta wannan  Kalidou Koulibaly da Raheem Sterling sun bugawa Chelsea wasan Premier league na farko da kafar dama

 

Da yawansu dai sun bayyana rashin abin yi da rashin wanda zai dauki nauyin rayuwarsu a matsayin dalilin da yasa suke karuwanci.

 

Sun nemi tallafin gwamnati dan ta basu sana’ar da zasu kama su daina wannan masha’a.

 

Gwamnatin jihar Bauchi dai a baya ta dauki nauyin aurar da karuwan da kuma baiwa wasu daga cikinsu sana’o’i, saidai da yawa daga cikinsu basu amfana da wannan tsari ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.