fbpx
Monday, December 5
Shadow

Abin tausai:”Yanda nayi haukar karya na wata tara dan tseratar da ‘ya’yana daga hannun ‘yan Boko Haram”>>inji wannan matar

Wannan baiwar Allahn me suna Zainab da diyarta, wadda gata can za’a iya hangota a zaune kan taga, sun samu sun tsallake cin zarafin mayakan Boko Haram ne ta hanyar dabarar da ita Zainab din tayi na haukan karya, har na tsawon shekara guda kuma ta boye diyartata a cikin magudanar ruwa, bayan da  Boko Haram din suka kwace garinsu na Madagli daga hannun sojoji.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Kamar yanda kafar watsa labarai ta The Guardian ta ruwaito, Zainab ta bayar da labarin ga manema labarai a sansanin gudun hijira na garin Gwoza inda yanzu take zaune.

Tace a lokacin da ta ga mayakan Boko Haram din sun kwace iko da garin nasu kuma sunata kashe mutane dake kokarin guduwa daga garin, sai tayi dabarar yin haukan karya, ta boye diyarta, Hassana wadda take tunanin ‘yan boko haram din zasu iya daukarta a matsayin mata a cikin magudanar ruwa dake cikin gidan, sannan ita kuma ta kwance gashin kanta, ta gogawa jikinta datti, tayi shiga tsirara-tsirara kamar dai mahaukaciya, ta fara haukan karya.
Haka ‘yan Boko Haram din suka zo suka kashe mijinta suka gama dube-dubensu basu ga komai ba suka fita, basu taba-taba ita da’ya’yanta biyu kanana saboda sunga kamar mahaukaciyace.
Bayan kwana biyu, sukaji labarin cewa haukan karyane take, lafiyarta kalau kuma tana da diya budurwa, haka suka dawo suka mata dukan Duniya, amma taki yin magana ta cigaba da haukan karya, suka duba ko’ina basu ga hassana diyartaba, suka dawo suka tsare kananan ‘ya’yanta, suka tambayesu, ko maman tasu haukan karya take?.
Yaran suna kuka, suka gayawa ‘yan Boko Haram din cewa mahaifiyarsu tana fama da ciwon hauka, ya dade, dama takan je Asibiti a Maiduguri a bata magani, amma ta dade bata jeba, ‘yan Boko Haram din sun taba kashe wata mahaukaciya a baya, abin ya shafesu, saboda haka suka sawa kansu dokar hana kashe mahaukata ko ‘ya’yansu, haka suka tafi suka bar Zainab, da kananan ‘yayanta, ita kuma ta cigaba da haukan karya.
Diyarta Hassana kuwa tana can cikin magudanar ruwa, saidai ta mika mata abinci da ruwa daga waje, haka suka rayu har tsawon watanni tara, lokacin da sojoji suka kwace garin na Madagali daga hannun ‘yan boko Haram din.
Da farko sojoji sun tambayeta ko ita matar mayakan Boko Haram din ce, tace musu a’a, duk da haka basu yarda ba, sai da ta basu labarin yanda tayi rayuwarta kuma taje inda ta boye Hassana suka ganta ta fito sannan suka yarda.
Ya Allah ka kaiwa duk musulmin dake cikin kunci tallafi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Tinubu zai kayar da Kwankwaso a Kano, kuma kuri'ar karamar hukuma daya tafi ta gaba dayan jihohin Inyamurai>>Inji Kwamishinan yada labarai na Kano, Muhammad Garba

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *