‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da fasinjoji a harin da suka kaiwa jirgin kasa na Kaduna sun saki sabon bideyo suna lallasar mutanen.
Inda daya daga cikin mutanen ya nemi agaji wurin sauran kasashen duniya cewa su taimake su tunda gwamnatin Najeriya ta gaza.
Yanzu kimanin watanni hudu kenan da ‘yan bindigar suka yi garkuwa dasu amma gwamnatin tarayya bata ceto ba.
Kuma a cikinsu hadda yara kanana da kuma tsaffi mata da maza.