fbpx
Friday, August 12
Shadow

Abin tausayi:”ko biliyan zaku bamu bama so saboda ba zata dawo mana da yaranmu ba”:Iyayen yaran da direba ya kashe suka koka domin har yanzu ba’a dauki mataki ba

Mahaifan wasu yara guda biyu mace da namiji, Olayinka da Oluwadamilola sun koka bayan direban babbar motar daya kashe masu yaransu har yanzu yana yawo a gari ba tare da an yanke mai hukunci ba.

mahaifin yaran, Opeyemi ya bayyana cewa yaran suna hanyarsu ta zuwa shagon mahaifiyarsu ne direban ya buge su, kuma ya gudu ba tare daya tsaya ya taimake su ba yayin da yaran suka mutu kafin su karasa asibiti.

Yan sanda sun kama direban mai suna Mashood Badamasi sun kai shi kotu amma daga bisani an bayar da belinsa, kuma mahaifan direban basu taba sun baiwa iyayen yaran hakuri ba akan abinda ya faru.

Karanta wannan  Kwalejin kimmiya da fasaha ta YABATECH ta hana dalibai sanya slippers zuwa makaranta

Sai dai su turo masu mutane cewa nawa suke bukata a basu. Kakar yaran itama ta rasu sanadiyyar hakan yayin da mahaifiyar yaran kullun itama tana hanyar zuwa asibiti saboda ta kamo da wata cutar.

Mamema labarai na PUNCH sun kira mai magana da yawun yan sanda na jihar Ogun amma yace ba zai iya cewa komai akan lamarin ba, domin an mika shi kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.