fbpx
Sunday, June 26
Shadow

Abinda shugaba Muhammadu Buhari ya fadawa ‘yan takarar APC a filin zaben fidda gwani na shugaban kasa

Shugaba Muhammadu Buhari yayi kira ga ‘yan takarar APC dake fafatawa a filin Eagle Square na Abuja wurin samun tikitin jam’iyyar na tsayawa takarar shugaban kasa.

Inda yace su hada kawunansu wuri guda su fitar da dan takara amintacce kuma na gari da zai yi nasara akan abokan hamayya a zaben shekarar 2023.

Sannan shugaban ya kara da cewa yana kira ga wa’yanda sukayi nasara da kuma wa’yanda suka fadi su hada kansu su cigaba da mu’amalantar juna kar a samu rabuwar kawuna.

Leave a Reply

Your email address will not be published.