fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Abinda wani alaramma, Abdulrashid ya kama matarsa me ciki na yi, ya saka mutane mamaki

Wani malamin Addinin Islama,  Abdulrashid Olalere ya zargi matarsa da cin amanarsa, inda yace ya kamata turmi da tabarya da wani kato, duk da cewa tana da ciki.

 

Ya bayyanawa kotun Mapo dake Garin Ibadan haka, kuma bayan da kotun ta gamsu da bayaninsa, ta raba auren nasu.

 

Matar ce dai ta kai karansa kotu, amma mijin, Abdulrashid ya mata wannan tonon silili inda yace kuma ta yi yunkurin guduwa da masoyin nata.

 

Yace a lokacin da ya kama Maryam na cin amanarsa, tana dauke da ciki wata 4. Hutudole.com ya fahimci cewa Malam Abdulrashid yace ya yafe mata suka ci gaba da zama, inda har kwarton da ya kamata dashi yayi ikirarin cewa cikin matar nasa ne amma da suka je Asibiti aka yi gwaji sai aka ga akasin haka.

 

Kamfanin dillancin labaran Najeriya,NAN ya ruwaito cewa, Abdulrashid yace, dangine suka saka baki har ta kai ga ya ci gaba da zama da Maryam, amma duk da haka bata daina cin amanarsa ba, inda ya sake kamata da wancan Kwarton nata, suna son tserewa.

 

Maryam dai bata musanta zargin da mijin nata yayi ba inda itama ta zargeshi da cewa baya kulata yanda ya kamata.

 

A baya dai, hutudole.com ya ruwaito muku yanda wani magudanci ya kashe matarsa a jihar Naija.

 

Mai shari’a, Ademola Odunade ya bayyana cewa tun farko ba’a gina auren kan turbar data dace ba, inda ya kashe auren sannan ya nemi Malam Abdulrashid ya rika baiwa matarsa Dubu 5 duk wata na kula da dansa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.