fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Abinda ya faru a Mali ya dameni sosai, ya kamata a kakabawa sojojin da suka kwace mulkin takunkumi>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa juyun mulkin da ya faru a kasar Mali ya dameshi sosai inda yayi kira da a sako shugaban kasar, Ibrahim Boubacar Keita da membobin gwamnatinsa da aka kama.

 

Shugaban kasar ya bayyana hakane a zaman ganawar da aka yi tsakanin kasashen Membobin ECOWAS a jiya, Alhamis. Hutudole ya kawo muku Yanda aka yi zaman ganawar a jiya inda shugaba Buhari ya halarta ta kafar sadarwar zamabi daga Abuja.

Shugaban yac koda murabus din da shugaba Keita yace yayi, tursasa masa aka yi dan haka ya kamata a hada kai a kakabawa sojojin da suka yi juyin mulkin takunkumi dan hakan yasa su mayarwa da shugaban kasar Mukaminsa.

Karanta wannan  Ba karamar dama na baka ka zama mataimakina ba kuma kar kayiwa kudu maso gabashin kasar nan asara, Kwankwaso ya fadawa Obi

 

Za’a aika tsohon shugaban kasar Najeriya,  Goodluck Jonathan da Jean Claude su kaiwa sojojin kasar Malin sakon matsayar da ECOWAS ta dauka.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.