fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Abinda ya faru tsakanin Gwamnan jihar Kaduna da wani me zaginshi kafafen watsa labarai: Karanta zaka karu

Akwai wani matashi a jihar Kaduna da aka bayyana sunanshi da ja’afar wanda a kullun rana ta Allah bashi da abinyi sai zagin gwamnan jihar,Malam Nasiru El-Rufai , shi ba adalin shugaba bane kuma cinye kudin mutane kawai yake, a gidajen rediyo, talabijin da kafafen sada zumunta  na yanar gizo. Wata rana sai gwamnan yasa a kira mishi ja’afar yazo gidan gwamnati.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Kuma ya gayamai cewa kada ya damu ya dauko hayar Keke-Napep/Adai-daita sahu/Agwagwa da buje idan yazo gidan gwamnatin shi gwamnan zai biya kudin.

Ai kuwa Ja’afar yana doki ya shirya ya tafi gidan gwamnati.
Da ya je sai ya shiga ciki ya amsowa me abin hawan kudinshi, sai gwamna El-Rufai ya baiwa Ja’afar dubu dari biyu yace ya baiwa me abin hawan saboda shima ya inganta sana’arshi tunda yau Allah ya kawoshi gidan gwamnati, Ja’afar ya fita ya dawo ya cewa gwamna ya sallami me abin hawan.
Gwamna ya tambayi Ja’afar yaya me abin hawan yayi da ya bashi kudin sai yace ai yayi murna sosai harda hawayen murna ya zubar.
Ashe gwamna ya sa a tsayar da me abin hawan da ya kawo ja’afar ba tare da sanin shiba, sai yasa aka shigo dashi ciki, ya tambayeshi nawa ja’afar ya bashi kudin sallama? Me abin hawan yace dubu biyu.
Nan Ja’afar yayi tsuru-tsuru, ido ya raina fata, Gwamna ya kalleshi yace toh Malam Ja’afar kullun kana zagina a gidajen watsa labarai cewa ni ba adalin shugaba bane kuma ina cinye kudin mutane, yau gaka cikin abinda baifi mintuna biyarba kayi cuci mutum.
Gwamnan ya dauko makulli ya nunawa ja’afar wata dalleliyar, sabuwar mota yacemai kaga wannan nayi niyyar in baka kuma har inyi aiki tare dakai da ace kana da gaskiya amma tunda haka kake kaje sai an jima.
Haka za’afar ya fita zugwi-zugwi, jiki ba nauyi.
Babu tabbacin wannan labari da gaskene saboda majiyar da akajishi bata da ingancin da za’a yadda da ita dari bisa dari amma saboda darasin dake tattare da labarin, shiyasa aka bayar dashi, idan bamu mantaba muna yara ana mana tatsuniyoyi wadanda wasu sun faru wasu kuma kirkirarsu akayi dan isar da sako.(gwamnan jihar Kadunan ya karyata wannan labari).
Akwai wani mawaki dake cewa wani mutum wai ya dena damuwa dan ana kiranshi da maye, duk wanda ya samu nama shima mayene.
Mafi yawancin mu da wuya mu iya tsallake irin jarabawar da akawa Ja’afar, shiyasa irin mu irin shuwagabanninmu Allah yasa mu dace, ya kuma bamu ikon gyarawa da iyawa duk wanda zamuyi wata mu’amala dashi adalci.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Tura ta kai bango: kalli bidiyon yanda 'yan Inyamurai suka fara kama 'yan IPOB suna kashewa

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.