fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Abubuwa basa tafiya daidai a Najeriya>>Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Janar Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, abubuwa basa tafiya yanda ya kamata a Najeriya.

 

Obasanjo ya bayyana hakane a wajan taron wata Coci a Abeokuta inda yace matsalolin kasarnan sai an hada da addu’a.

 

Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya bayyana cewa, Obasanjo yace ba Najeriya bane kadai kasar da ake samun irin wannan matsala.

 

Yace Duniyace gaba daya. Yayi fatan cewa nan gaba abubuwa zasu canja a kasarnan. Obasanjo wanda ya dade yana caccakar gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari yace qna bukatar Shuwagabannin masu gaskiya da rikon amana dan gyara Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.