Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto wanda kuma yake neman takarar shugabancin Najeriya a jan’iyyar PDP yace Najeriya na tafiya kamar ba shugabanci.
Tambuwal ya bayyana hakane a Yenagoa dake jihar Bayelsa inda yace shiyasa suke kokarin ganin sun zo dan kawo dauki a Najeriya.
Yace matsalar tsaro ta yawaita, babu yankin kasarnan dake zaune lafiya.
Yace a halin da ake yanzu babu maganar zuba jari ko kuma ci gaba, abinda ake nema shine zaman lafiya tukuna.